Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeBusiness2021 05 02Article 450556

BBC Hausa of Dimanche, 2 Mai 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Aguero, Salah, Ramos, Pirlo, Flick, Toney, Tuanzebe

Sergio Aguero, dan wasan Manchester City Sergio Aguero, dan wasan Manchester City

Everton ta bi sahun Chelsea da Leeds United da Tottenham da Barcelona da kuma Inter Milan wajen zawarcin dan wasan gaba na Argentina Sergio Aguero, wanda kwantiraginsa da Manchester city zai kare a bazara. (Jaridar Daily Star ta Lahadi)

Dan wasan gaba na Masar Mohamed Salah ya ce shugabannin Liverpool ba su yi masa magana ba dangane da tsawaita kwantiragin zamansa a kungiyar ba. Wa'adin zaman dan wasan mai shekara 28 na yanzu a kungiyar zai kare ne a 2023. (Tashar Sky Sports)

Arsenal ta yi amanna za ta iya dauko dan wasan tsakiya na Brighton da Mali Yves Bissouma mai shekara 24 a kan fam miliyan 30. (Jaridar Daily Star Sunday)

Har yanzu dan bayan Sifaniya Sergio Ramos, mai shekara 35, na cike da fatan Real Madrid za ta tsawaita kwantiraginsa da karin shekara biyu. Kungiyar dai ta masa tayin karin shekara daya ne, a kan wa'adin zamansa da zai kare a bazaran nan. (Jaridar Marca)

Kwantiragin mai tsaron ragar Italiya Gianluigi Donnarumma da AC Milan zai kar e a bazara, kuma tuni wakilin dan wasan, Mino Raiola, ya tattauna da Juventus kan tafiyar Golan mai shekara 22 can. (Jaridar Calciomercato)

Kociyan Juventus Andrea Pirlo ya mayar da martini ga rade-radin da ake yi game da zamansa a kungiyar, inda ya ce ya yi Magana da masu kungiyar, kuma sun ce ba su da wata damuwa game da aikinsa. (Jaridar Goal)

Mai horad da Bayern Munich Hansi Flick na son zama kociyan tawagar kasar Jamus, idan Joachim Low ya tafi bayan gasar cin kofin Turai ta bazaran nan, kuma y ace bas hi da sha'awar karbar aikin Tottenham. (Sport1)

Tottenham ta bi layi wajen zawarcin dan wasan gaba na Brentford kuma dan Ingila Ivan Toney, mai shekara 25. (Jaridar Football Insider)

Kociyan Arsenal Mikel Arteta a shirye yake ya bayar da dama ga dan wasan tsakiya na Ingila Joe Willock mai shekara 21, wanda yanzu yake zaman aro a Newcastle United, ya nuna kansa a Arsenal din. (Shields Gazzette)

Haka kuma Artetan ya ce Arsenal za ta yarda ta tattauna a kan batun kara tsawon kwantiragin dan wasan tsakiya na Ingila mai shekara 20 Emile Smith Rowe a kungiyar. (Tashar Sky Sports)

Aston Villa na shirin zawarcn dan bayan Manchester United, dan Ingila Axel Tuanzebe, mai shekara 23, wanda a baya ya taba zaman aro a kungiyar.(Jaridar Football Insider)

Wakilin dan bayan Sifaniya Eric Garcia na dab da cim ma yarjejeniya wadda za ta kai ga tafiyar dan wasan mai shekara 20 Barcelona, bayan kwantiraginsa da Manchester City yak are a bazara. (Jaridar Mundo Deportivo)