Vous-êtes ici: AccueilRéligion2021 05 04Article 450598

BBC Hausa of Mardi, 4 Mai 2021

Source: BBC

Greenfield: Ƴan Twitter sun buƙaci gwamnati ta ceto ɗaliban Kaduna

Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufa'i, Gwamnan jihar Kaduna

Batun makomar ɗaliban Jami'ar Greenfield ta Kaduna a arewacin Najeriya ya ja hankalin ƴan Najeriya bayan da ƴan bindigar da suka sace su suka yi barazanar halaka su idan har ba a biya kuɗin fansa ba.

Ƴan bindigar da suka sace ɗaliban sun ba gwamnatin Kaduna wa'adin ƙarshe ta biya kuɗi ko su halaka su.

Ƴan bindigar sun kashe biyar daga cikin ɗaliban, yayin da har yanzu akwai aƙalla ɗalibai 17 a hannun ƴan bindigar.

Wannan na zuwa yayin da Iyayen ɗaliban kwalejin gandun daji a Kaduna suka gudanar da zanga-zanga a harabar ginin majalisa a Abuja domin neman a ceto ƴaƴansu da ƴan bindiga suka sace a watan Maris.

Ɗalibai 39 aka sace amma an saki 10 daga cikinsu.

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya sha nanata cewa ba zai sulhu da ƴan bindiga ko ya biyan kuɗin fansa ba.

Damuwa da fargaba game da makomar ɗaliban a hannun ƴan bindiga ne ya ja hankalin ƴan Najeriya a shafukan sada zumunta.

An ƙirƙiri Maudu'in jami'ar Greenfield (#Greenfielduniversity) a shafin Twitter domin kiran ceto ɗaliban da aka sace.

Maudu'in ya kasance ɗaya daga cikin wanda aka fi tattaunawa a Najeriya, inda mutane ... suka yi tsokaci akai.

Me ƴan Najeriya ke cewa?

Ana amfani da maudu'in #Greenfielduniversity a Twitter domin kiran ceto ɗaliban na Kaduna.

Ƴan Najeriyar na kira ne ga hukumomin gwamnatin Tarayya da hukumomin tsaro da kuma na jihar Kaduna da matsalar ta shafa su ceto ɗaliban.






Wasu kuma addu'ar mafita suka dinga yi wa ɗaliban

@JudiboyBaby ya ce: A matsayi na ckakken ɗan Najeriya na gaskiya, muna addu'a ga ɗaliban Jami'ar Greenfield. Allah Ya kare su kuma Ya sa gwanati ta ɗauki mataki kan hare-haren da ake fama da su.

An saki dama daga cikinsu bayan tattaunawa tsakanin hukumomi da ƴan bindigar masu satar mutane. Ana tunanin an biya kuɗin fansa kafin sakinsu.

Amma gwamnatin Tarayya da gwamnatin Kaduna suna kan manufar adawa da tattaunawa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai domin a cewarsu tattaunawar da biyar kuɗin fansa zai ƙarfafa masu gwiwa su ci gaba da aikata laifi.

Sai dai ƙoƙarin da jami'an tsaro suka yi na kuɓutar da ɗaliban da aka sace zuwa yanzu ya ci tura.