Vous-êtes ici: AccueilRéligion2021 04 19Article 450295

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Makoman Mourinho da Pogba da Sterling da Traore Varane Abraham

Kocin Tottenham Lourinho tare da dan wasan kungiyar Son Kocin Tottenham Lourinho tare da dan wasan kungiyar Son

Ana kyautata zaton da ƙyar kocin Tottenham Jose Mourinho ya ci gaba da zama a ƙungiyar zuwa kaka mai zuwa, yayinda ƙungiyar ke fatan samun gurbi a gasar zakaran turai na 2021 zuwa 2022.(Football London)

Ɗan wasan tsakiya a Faransa, Paul Pogba na son a biya shi £500,000 - a kowanne mako - kafin ya amince da yarjejeniyar Manchester United, yayinda Real Madrid da Paris St-Germain da Juventus aka sanar da su kuɗaɗen da ɗan wasan mai shekara 28 ke buƙata idan suna son sayen sa. (Daily Star on Sunday)

Ɗan wasan gaba a Manchester City Raheem Sterling, mai shekara 26 na sake ƙwadayin koma wa Real Madrid, yayinda ya yi fama da kansa a wasanninsu na baya-bayanan da tawagar ta Ingila. (Daily Star on Sunday)

Wolves na son raba gari da ɗan wasanta Adama Traore domin samun kuɗaɗen kula sabon kwantiragi kuma £30m ya ishe kowanne kulob cimma yarjejeniya da ɗan wasan mai shekara. (Football Insider)

Chelsea za ta fafata da Manchester United wajen sayen ɗan wasan Real Madrid kuma ɗan Farans, Raphael Varane, mai shekara 27. (Bild journalist Christian Falk, via Sunday Express)

Makomar ɗan wasan Ingila Tammy Abraham's a Chelsea na cikin rashin tabbas bayan kocinsu Thomas Tuchel yaƙi sanya ɗan wasan mai shekara 23 a wasan ɗab da na ƙarshe da suka yi nasara akan Manchester city. (Mail on Sunday)

AC Milan ta shaidawa Chelsea aniyarta na ci gaba da riƙe Fikayo Tomori da yanzu haka ke mata wasa a matsayin ɗan aro. (Football Insider)

Aston Villa da Crystal Palace na zawarcin Ruben Loftus-Cheek ɗan shekara 25 da ke taka leda Chelsea, amma yanzu haka yake wasa a matsayin ɗan aro a Fulham. (Teamtalk)

Leeds United ta ƙoƙarin ganin ta dauko Nicolas Tagliafico, ɗan Argentina wanda kwantiraginsa ba zai ƙare a Ajax ba sai shekara ta 2023. (Sunday Mirror)

West Ham na sake ƙwadaituwa da ɗan wasan Sparta Prague wato Adam Hlozek, matashi ɗan shekara 18 asalin Jamhuriyar Czech. (90 Min)

Kocin Newcastle United Steve Bruce yace zai so ya cigaba da rikeJoe Willock da ke buga tsakiya, wanda yanzu haka yake zaman aro a ƙungiyar daga Arsenal. (Metro)

Ɗan wasan Norwich mai shekara 24, Emiliano Buendia, wanda ake alaƙantawa da Arsenal, yace yana da ɗamar barin ƙungiyar tun a watan Janairu amma ya zaɓi ci gaba da zama domin taimaka mata kai wa matakin firimiya. (Metro)