Vous-êtes ici: AccueilSport2021 05 15Article 450803

BBC Hausa of Saturday, 15 May 2021

Source: BBC

Isra'ila ta kai hari sansanin 'yan gudun hijira a Gaza

Hare-haren Isra'ila akan 'yan gudun hijira da ke Gaza ya kashe akalla mutum bakwai Hare-haren Isra'ila akan 'yan gudun hijira da ke Gaza ya kashe akalla mutum bakwai

Ma'aikatar lafiya a Falasdinu ta ce hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira da ke Gaza ya kashe akalla mutum bakwai.

Wani jami'i ya ce cikin wadanda suka mutu akwai mace guda da kananan yara hudu, wadanda ke cikin gidanus a cikin sansani 'yan gudun hijira na Al- Shati da ke gabashin Gaza.

Isra'ila dai ba ta ce uffan kan wannna batu ba. Sai dai mayakan Falasdinawa sun maida martani ta hanyar harba makaman roka birnin Beersheba da ke Isra'ila.

kusan mutane 140 ne suka mutu a Gaza tun bayan fara rikicin a ranar Litinin, ya yin da makaman rokar da Falasdinawa suka harba ya hallaka 'yan Isra'ila takwas.Ma'aikatar lafiya a Falasdinu ta ce hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai sansanin 'yan gudun hijira da ke gaza ya kashe akalla mutum bakwai.

Ci gaba da kai hare-hare ta sama da sojojin Israila ke yi, ya janyo tashin hankali a yamma da gabar kogin Jordan da yammacin birnin Kudus.

Akalla Falasdinawa goma sha daya ne suka mutu, a taho mu gama tsakaninsu da jami'an tsaron Isra'ila. A cikin Isra'ila kuma, ana ci gaba da gwabzawa tsakanin Yahudawa da Larabawa a birane daban-daban.

A birnin Jaffa an kona wasu yara Larabawa a lokacin da Yahudawa suka cinnawa gidansu wuta ta hanyar harba bam din da aka hada da fetur.

Harwayau an yi ta zanga-zanga a iyakar kasar da Jordan da kuma Labanun, inda hari ta sama da Isra'ila ta kai ya kashe wani Ba'falasdine.