Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 21Article 450893

BBC Hausa of Vendredi, 21 Mai 2021

Source: BBC

Saudiyya ta yarda 'yan kasashen waje su je aikin Hajjin bana

Saudiyya ta yarda 'yan kasashen waje su je aikin Hajjin bana Saudiyya ta yarda 'yan kasashen waje su je aikin Hajjin bana

Za a bar maniyyata daga fadin duniya su je aikin Hajji a wannan shekarar, tare da tabbatar da bin tsauraran dokokin domin kiyaye yaduwar korona a masarautar, kamar yadda wani rahoton jaridar Al-Watan ta rawaito.

Wannan matakin na zuwa ne bayan hukuncin da hukumar Hajji da Umara ta kasar ta yanke a ranar 9 ga watan Mayu cewa ya kamata a bar mahajjata su yi aikin amma da sharudan hukumomin lafiya.

A farkon wannan watan ne, Ma'aikatar Lafiya ta Saudiyya ta ce za su ci gaba da aiki ba dare ba rana domin tabbatar da cewa an kiyaye lafiyar duk wanda ya je aikin ibada a kasar.

Sabuwar sanarwar ba ta fayyace yawan mutanen da za a bari su yi aikin Hajjin na bana ba, sannan ba a faɗi kasashen da za su je ba.

Amma tuni kasashe irin Najeriya ke sa rai tare da fatan za a bar maniyyatanta zuwa Hajjin na bana.

Sai dai ma'aikatar ta ce za ta sanar da hanyoyin kare kai da za a bi domin kiyaye yaduwar korona daga baya.

Musulmi sama da miliyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji a ko wacce shekara daga fadin duniya.

Amma saboda annobar korona aka rage adadin zuwa 1,000 a bara kuma su ma mazauna Saudiyyan ne kawai.

Annobar cutar korona ta janyo an samu sauye-sauye da dama na yadda ake gudanar da ibada a Makka da MAdina kamar shiga sallah Harami da Dawfi da Safa da Marwa da sauran su.