Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 19Article 449748

BBC Hausa of Friday, 19 March 2021

Source: BBC

Dortmund ta dauki Soumaila Coulibaly daga PSG

Soumaila Coulibaly Soumaila Coulibaly

Borussia Dortmund ta kammala daukar matashin dan wasa, Soumaila Coulibaly daga Paris St Germain, kamar yadda kungiyar Jamus ta sanar.

Tuni kuma dan wasan ya saka hannu kan doguwar yarjejeniya don komawa buga gasar Jamus.

Mai shekara 17 mai tsaron baya daga tsakiya, wanda ya fara taka leda daga matasan PSG, zai koma Dortmund a kakar 2021-21.

Coulibaly wanda har yanzu bai yi wa babbar kungiyar wasa ba, duk da atisaye da yake yi da ita a koda yaushe na jinyar rauni da ya yi tun cikin watan Fabrairu.